An tsare 'yan Nigeria 1,000 a Saudiyya

Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Wasu 'yan Najeriya da kuma 'yan Jamhuriyar Nijar da hukumomin Saudiyya ke tsare da su bayan da hukumomin suka fara tasa keyar 'yan ci-rani da ba su da takardun izinin zama cikin kasar, sun ce suna cikin wani mawuyacin hali.

Galibi wadanda ake tsare dasu sun ce sun galabaita sakamakon rashin isasshen abinci da kuma tsananin sanyi a wurin da ake tsare dasu.

Kimanin watanni bakwai kenan da kasar Saudiyyar take tankade da rairayar bakin hauren da basu da cikakkun takardun zama a kasar.

Wani dan Najeriya dake cikin wadanda ake tsare dasu da ba ya so a ambaci sunansa, ya shaidawa BBC cewar "kawo yanzu hukumomin Najeriya basu ziyarcesu ba don tallafa musu".

'Yan Nigeria fiye da 1,000 ne ake tsare dasu a wani wurin ajiye kayayyaki a Saudiyya dake tsakanin Makka da Jeddah wanda kuma suka shafe kusan makwanni.

Karin bayani