Kananan jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga a Najeriya

Image caption Filin Jirgin Saman Birnin Legas

Yanzu haka kananan jiragen saman haya da ke tashi a Najeriya sun dakatar da zirga zirgarsu a kasar bayan bullo da wani sabon haraji da hukumar kula da sararin samaniya a kasar ta yi.

Sabon harajin dai na bukatar duk wani mai karamin jirgi da aka yi wa rijista a cikin kasar da ya biya dalar Amurka 3,000 kafin tashi yayin da wanda aka yi wa rijista a wata kasar waje zai biya dala 4,000.

Kungiyar Masu Jiragen Sama a kasar ta ce kananan jiragen ba za su ci gaba da jigilar fasinjoji ba har sai gwamnatin ta janye harajin.

'' Babu inda ake wannan a ko'ina a duniya. Ina tabbatar maka idan kana Turai ka tashi tafiya(da jirginka) abin da za ka biya kawai kudin sauka da na tashi daga filin jirgi'', in ji Mataimakin Sakataren kungiyar Alhaji Muhammed Tukur.