Najeriya ta karyata zargin 'yan kasarta a Saudiyya

Baki 'yan kasashen waje a Saudiyya
Image caption Tun da farko hukumomin Saudiyyan sun bai wa bakin wa'adin sabunta takardunsu

Mahukuntan Najeriya sun musanta zargin cewa, ba sa kula da 'yan kasar da suka sami kansu cikin halin kaka-nika-yi a wurin da suke tsare a Saudi Arabia.

Yayin da Saudi Arabiyar ke cigaba da korar 'yan kasashen wajen da ba su da cikakkun takardun zama a kasar, ko kuma na aiki.

A wata hira ta waya da wani dan Najeriya a Saudiyya yayi da BBC, ya ce kawo yanzu ba wani jami'in Najeriya da ya ziyarce su, ga shi kuma su na fama da yunwa da rashin lafiya.

Jakadan Najeriyar a Jeddah, Alhaji Ahmed Umar, shi ne ya musanta zarge-zargen da cewa suna bakin kokarinsu na kaiwa ga mutanen illa dai suna da yawa ne.

Karin bayani