'Ilimi na kara tabarbarewa a Afrika'

Image caption Yarinya 'yar makaranta a Nigeria

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a duniya, Transparency International ta kaddamad da wani rahoto kan na'ui da dama na cin hanci da rashawa wadanda suka dabaibaye harkar ilimi a nahiyar Afrika.

Rahoton, ya yi nunin cewa almubazzaranci da kudaden jama'a da bayar da takardun shedar kammala karatu ta boge da rashin zuwan malamai a makarantu ko kuma cin zarafin 'yammata da malamai ke yi a makarantu duka na'o'i ne na cin hanci da rashawa da fannin ilimin ke fuskanta.

Kungiyar ta Transparency ta ce, wadannan matsaloli suna matukar barazanar wargaza tsarin ilimi a nahiyar ta Afrika.

A bangaren Nigeria tabarbarewar harkokin ilimi a makarantun gwamnati ya sa jama'a dake da hali zabar sanya 'ya'yan su a makarantu masu zaman kan su da nufin samun ilimi mai nagarta.

Sai dai hukumomi na cewa da dama daga irin wadannan makarantun ana gudanar da su ba bisa ka'ida ba.

Wasu bayanai dai ma cewa hukumomin jihar Kaduna sun rufe irin wadannan makarantun sama da 2500, yayin da hukumomin jihar Kano kuma suka ce sun gano makarantun jeka na yi ka sama da 2000.

Karin bayani