"Dr Nazeef ba dan Boko Haram ba ne"

'Yan Boko Haram
Image caption 'Yan Boko Haram

Iyalan malamin jami'ar nan, kuma mai wa'azin addinin Islama da jami'an tsaron Najeriya suka kama a makonnin baya, bisa zargin cewa shi jami'i ne na Boko Haram, sun karyata zargin da ake masa.

A jiya ne dai hukumar 'yan-sandan ciki ta kasar wato SSS ta gabatar da Dr Muhammad Nazeef, tare da wasu mutanen hudu ga manema labarai, inda ta ce 'yan Boko Haram ne.

Dokta Muhammad Nazeef dai shi ne daraktan makarantar Sakandare ta Al-bayan da ke birnin Jos, kana malami a jami'ar jihar Kogi.

Hukumomi sun ce yana tsara hare-hare a jihar ta Kogi, yana kuma daukar mutane aiki a cikin kungiyar ta Boko Haram.