'An bautar da wasu mata a Birtaniya'

Image caption Firaiministan Birtaniya, David Cameron

'Yan sandan Birtaniya sun ce, sun kubuto wasu mata uku daga wani gida a nan London inda bisa ga dukkan alamu aka tsare matan ba da son ransu ba tsawon shekaru talatin.

An dai bayyana cewa dukkan matan suna cikin hali na jigata.

Tuni dai aka kama wata mata da kuma wani mutum 'yan shekaru kimanin sittin yayin da aka soma bincike a kan zargin sa bauta.

Matan da lamarin ya shafa dai 'yan tsakanin shekaru talatin zuwa sittin da tara sun fito ne daga Birtaniya da kuma da Ireland da kuma Malaysia.

Karin bayani