An nada sabon Firai Minista a Chadi

Djimrangar Dadnadji
Image caption Mulkin Kasar Chadi ya fi karfi a hannun Shugaba Idriss Deby

An nada sabon Firai Minista a Chadi- sa'oi bayan magajinsa ya yi murabus saboda yana fuskantar kuri'ar yanke kauna.

Gidan Talabijin din Kasar dai ya bayyana sunan Kalzeubet Pahimi Deubet- masanin tattalin arziki wanda ke rike da kamfanin audugar gwamnatin Kasar.

Ya dai maye gurbin Djimrangar Dadnadji, wanda aka yi wa gwamnatinsa garanbawul har sau biyar, tun lokacin da ya hau matsayin Firai Minista a farkon shekarar da ake ciki.

Masu aiko da rahotanni sunce mulkin Kasar ya fi karfi a hannun Shugaba Idriss Deby, wanda ya shafe fiye da shekaru ashirin yana mulkar Kasar.

Karin bayani