Tattaunawa kan nukiliyar Iran ta Kankama

zaman tattaunawa
Image caption An tsara tattaunawar ta birnin Geneva ta ci gaba har zuwa ranar Jumu'a

An soma tattaunawa gadan-gadan a birnin Geneva kan shirin nukiliya na Iran.

Manyan kasashen duniya shida da suka hada da Amurka na neman cimma wata yarjejeniyar wucin gadi.

Wadda a karkashinta Iran za ta takaita shirinta na inganta sinadarin Uranium domin su kuma kasashen su sassauta takunkumin da suka sanya mata.

Bangarorin biyu sun ce tattaunawar share fagen da aka yi ranar Laraba ta yi armashi.

Sai dai Iran ta ce ba za ta ja da baya ba wajen aiki da hakkin da take da shi na sarrafa makamashin nukiliya.

Karin bayani