Likitoci sun bukaci Jonathan ya huta

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Likitoci a London sun bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya huta zuwa wani dan kankanin lokaci bayan da suka duba lafiyarsa.

Shugaban Nigeriar ya kasa halartar bude taro kan batun zuba jari saboda rashin lafiyar.

Sanarwar da fadar Shugaban Kasar ta fitar wadda Dr Ruben Abati ya sanya wa hannu, ta ce rashin lafiyar ba mai tsanani ba ce, kuma likitoci sun duba shi ne kawai a matsayin riga kafi.

Wannan sanarwar ta rashin lafiyar shugaba Jonathan ta zo da bazata saboda ba kasafai shugabanni a Afrika ke ba da cikakkun bayanai ba a kan koshin lafiyarsu.

A watan Mayun wannan shekarar ma, Shugaba Jonathan bai gabatar da jawabinsa ba a kan lokaci a wurin taron koli na kungiyar kasashen Afrika a Addis Ababa abinda ya janyo cece-kuce a kasar.

Daga bisani fadar Shugaban kasar ta ce, Mr Jonathan yana tattaunawa da wasu jami'ai ne shi yasa bai samu damar gabatar da jawabin a kan kari ba.

Karin bayani