Amurka ta matsu kan yarjajeniya da Afghanistan

Hamid Karzai, Shugaban Afghanistan
Image caption Hamid Karzai, Shugaban Afghanistan

Amurka ta yi kira ga Afghanistan da ta sa hannu a kan yarjajeniyar karshe game da wani sabon shiri na tsaro kafin karshen wannan shekarar.

Tun farko a yau Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce ba za'a sanya hannu akan yarjejeniya ta karshe akan sabon shirin hadin gwiwa ta fuskar tsaro tsakanin kasar da Amurka ba, har sai bayan zaben shugaban kasar da za'a yi cikin watan Afrilun badi.

Shugaba Karzai ya bukaci taron koli na shugabannin kabilun kasar da ake yi a birnin Kabul ya amince da yarjejeniyar, wadda zata bada dama ga dakarun Amurka su ci gaba da kasancewa a kasar har bayan shekara ta 2014.

Daga daga cikin manyan batutuwan da ke janyo takaddama shine: irin samamen da dakarun Amirka ke kaiwa a gidajen jama'a.

To amma shugaba Karzai ya gabatar masu wata wasika daga shugaba Obama, inda yake tabbatar da cewa, sojojin Amirka ba za su shiga gidajen jama'ar ba, sai fa idan ta kama dole.