Majalisar Wakilan Nigeria ta amince da karin dokar ta baci

shugaban majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal
Image caption 'Yan majalisar sun ce sun gamsu da dalilan bukatar kara wa'adin dokar ta-bacin

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar ta kara wa'adin dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Jihohin dai suna fama ne da hare-hare daga kungiyar jama'atu ahlissunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da boko-haram.

Tuni dai majalisar dattawan kasar ta amince da karin wa'adin.

Amma majalisar wakilan ta jinkirta har sai ta gana da hafsoshin tsaron kasar.

Karin bayani