Rikicin jami'yyar PDP ya ta'azzara

Image caption PDP dai ta fada rikici tun lokacin da wasu gwamnoni da manyan jami'anta suka balle

A Najeriya, shugabannin sabuwar PDP da suka hada da Alhaji Kawo Baraje da wasu mutane uku sun ce ba za su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar jam'iyyar PDP karkashin Bamanga Tukur ba.

Bangaren Bamanga Tukur din dai ya gayyaci jami'an sabuwar PDPn ne don jin bahasi daga gare su game da zargin da jam'iyyar ke musu na yi mata zagon-kasa, a ranar Laraba mai zuwa.

Sai dai daya daga cikinsu, Sanata Ibrahim Kazaure, ya ce ba za a yi musu adalci ba don haka ba za su gurfana a gaban kwamitin ba.

Ya kara da cewa babu wanda ya isa ya gurfanar da shi a gabansa a cikin 'yan bangaren Bamanga Tukur.

Tun a makon jiya ne kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya sanar da dakatar da su daga mukamansu.

Karin bayani