'Yan Shi'a sun kai hari Saudiyya

TaswirarSaudia da makwabtanta
Image caption Wasu rahotanni sun ce kawo yanzu ba a tabbatar da ikirarin kungiyar na kai harin ba

Saudi Arabia da Iraqi na gudanar da bincike kan wasu bama-baman roka shida da aka harba yankunan Saudiya da ke kusa da iyakar Iraqi da Kuwait.

Hukumomin Saudiyan sun ce basu san wanda ya harbo makaman ba kuma inda aka harbo su.

Sai dai wata karamar kungiyar gwagwarmaya ta 'yan Shia mai suna Dakarun Mukhtar ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar ta ce harin gargadi ne ga Saudiyya kan ta kiyayi shiga harkokin Iraqi.

A baya dai gwamnatin Iraqi da 'yan Shi'a suka mamaye ta bayar da sammacin kama shugaban kungiyar.