An tsare budurwa saboda fyade a Somalia

Image caption Mahukunta sun ce dole a bari hukunci ya yi halinsa

An tsare wata budurwa a Mogadishu, babban birnin Somali, bayan ta gayawa wata jarida cewa an yi mata fyade da karfin bindiga.

Shi ma dan jaridar da ya yi hari da budurwar, mai shekaru 19 a duniya, ma an daure shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da bincike kan batun.

Gwamnatin Somali ta ce dole a bari hukumomi su yanke hukunci a game da al'amarin.

A farkon wannan shekarar an yanke hukuncin zaman gidan yari na shekara kan wata budurwa da ta yi zargin an yi mata fyade da kuma dan jaridar da ta gaya wa, sai dai daga bisani an sake su bayan sun daukaka kara.

Karin bayani