Afghanistan na taro kan yarjejeniya da Amurka

Image caption Amurka ta yi barazanar janye sojojinta daga Afghanistan idan ba a kotunanta za a yi musu shari'a ba kawai.

Wakilai 2500 na al'ummomin Afganinstan sun soma wani taro a Kabul karkashin babbar majalisar shugabannin al'umomin kasar ta Loya Jirga domin duba wata yarjejeniyar tsaro da Amurka.

Da daren Laraba ma'aikatar harkokin wajen Afghanistan ta wallafa daftarin yarjejeniyar wadda a cikinta ta amince cewa za a yi wa sojan Amurkar Shara'a ne a kotunan Amurka a maimakon na kasar ta Afghanistan idan suka aikata laifi.

Sai dai dole ne sai majalisar ta Loya Jirga ta amince, haka ma ana neman wakilan su amince da sharadin cewa sojan Amurka za su ci gaba da kasancewa a kasar har bayan shekara mai zuwa.

Saboda sarkakiyar da ke ga yin amfani da harsuna uku a lokaci daya da kuma kasancewar wakilai da yawa ba su iya karatu ba, abubuwa da yawa sun dogara ne kan yadda Shugaba Karzai zai gabatar da daftarin yarjejeniyar.

Karin bayani