Amurkawa na tunawa da shugaba Kennedy

Marigayi shuagaba J F Kennedy
Image caption J F Kennedy na daga shugabannin Amurka da aka fi darrajawa

Za a sauko da tutoci kasa kasa sannan kuma a yi tsit na wani dan lokaci a Amurka domin tunawa da shekaru 50 da kisan gillar shugaba J F Kennedy.

Za a yi ta kada kararrawa a Dallas ta Texas inda aka kashe shugaban ranar 22 ga watan Nuwamba shekara ta 1963.

Yayin da Amurka ke shirin tunawa da shekaru 50 da kisan shugaban jama'ar kasar na tuna yadda suka ji labarin mutuwar tasa.

A watan Yuni na shekara ta 1963, Mr Kennedy ya gabatar da wani jawabi mai muhimmancin gaske a Berlin inda yake bayar da goyon bayan Amurka ga al'ummar Jamus ta Yamma.

Darektan cibiyar nazarin harkokin Amurka ta Arewa ta John F Kennedy da ke jami'ar Freie a Berlin, Winfried Fluck ya halarci wurin jawabin shugaban a lokacin yana matashi.

Ya ce, '' babban abin takaici ne da ya ratsa ni a lokacin da na ji labarin mutuwar shugaban bayan 'yan watanni.''