Shugaban Venezuela ya kama 'yan adawa

Nicolas Maduro
Image caption 'Yan adawa sun shirya yin zanga zanga a ranarAsabar

Shugaban Kasar Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da tsare wasu mambobin 'yan adawa su biyu gabanin zanga zangar da aka shirya yi yau Asabar.

Mr Maduro ya ce mutanen biyu na da niyyar tunzura jama'a, ta hanyar tsara cewa zasu sa mahaya babura 'yan adawa su sanya jajayen kaya wato launin jam'iyyar dake mulki a kasar.

Mafiyawancin mahaya baburan dai na goyan bayan gwamnati.

Tunda farkon makon da ake ciki ne aka baiwa Mr Maduro wani iko na musamman na gudanar da mulkin kasar ta hanyar dokar soji tsawon shekara guda, kuma zanga zangar ta ranar Asabar , an shirya tane dalilin abinda jagoran 'yan adawar Kasar Henrique capriles ya bayyana da cewa, ikon da Shugaban Kasar ya kwace

Karin bayani