APC ta ce za ta kauracewa ragowar zaben Anambra

APC
Image caption APC na neman a soke zaben gwamnan Anambra bakidayansa

Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta ce za ta kauracewa ragowar zaben gwamnan Jahar Anambra idan hukumar zaben bata soke zaben baki dayansa ba.

Kawo yanzu dai zaben gwamnan jihar Anambran da aka yi makon da ya gabata na ci gaba da janyo ce-ce ku-ce a Kasar .

Hukumar zaben kasar dai ta sanar da ranar 30 ga watan da muke ci a matsayin ranar da za'a sake gudanar da zabe a wasu mazabu dake cikin jihar.

Sanata Lawan Shu'iab shi ne mataimakin sakataren tsare tsare na kasa na jam'iyyar APC, kuma ya shaidawa BBC cewa idan ta kama 'ya'yan jam'iyyar za su yi takakkiya har zuwa hukumar zaben Kasar domin su tabbatarwa da hukumar cewa ba za su shiga zaben ba.

Jam'iyyar dai ta yi zargin cewar hukumar zaben Kasar ta zalunce ta.

Karin bayani