Shugaba Jonathan zai koma gida ranar Lahadi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Likitoci wadanda suka duba lafiyar shugaban Najeriya Goodluck Jonathan sakamakon matsanancin ciwon ciki da ya fuskanta bakatatan a nan London sun tabbatar da koshin lafiyarsa domin komawa gida ya cigaba da ayyukansa.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Ruben Abati ya fitar ta ce bayan cikakken bincike akan alamomin ciwon wanda likitoci suka baiyana da cewa ciwon ciki ne mai tsanani, likitocin a karshe sun hakikance shugaban baya bukatar a yi masa wani gagarumin aiki.

Sanarwar ta ce shugaba Jonathan zai koma Abuja ranar Lahadi da maraice zai kuma koma bakin aiki a ranar Litinin.

Shugaban ya sake godewa dukkan yan Najeriya bisa goyon baya da kuma addu'oin da suka rika yi masa ta samun sauki cikin hanzari bayan da aka bada sanarwar cewa bai ji dadi

Karin bayani