Yara fiye da dubu goma sha daya aka kashe a Syria

Yara a Syria
Image caption Mafiyawancin wadanda lamarin ya shafa, an kashe sune ta hanyar harba masu makaman igwa.

Wani sabon bincike da aka wallafa ya nuna cewa yara kanana fiye da dubu goma sha daya ne aka kashe a kusan shekaru ukun da aka shafe ana yakin basasa a Syria.

Binciken wanda Oxford Research Group ta gudanar, wanda kuma aka sakarwa BBC, ya nuna cewa mafiyawancin wadanda lamarin ya shafa an kashe sune ta hanyar harba masu makaman igwa .

Amma binciken ya kuma nuna cewa 'yan bindiga dadi sun hari Yara fiye da dubu- daya da gangan domin su hallaka su, kuma an kashe yara akalla dari daya, wasu ma 'yan shekara daya kachal a duniya ta hanyar azabtarwa.

Rahotan ya bukaci dukkanin bangarorin su kare rayukan kananan Yaran Syria, ya kuma yi kira da a hukunta wadanda suka aiwatar da munanan laifuka

Karin bayani