Rudani a yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran

Bisa ga dukkan alamu dai har yanzu akwai dan rudani akan matsayin Amurka da na Iran akan yarjejeniyar da aka cimma akan shirin nukiliyar Iran, musamman ma dangane da ko Iran tana iko cigaba da habaka makamashin Uranium.

Shugaban Iran, Hassan Rouhani yayi marhabun da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya dangane da shirinta na nukiliya.

Shugaban yace, abinda aka cimma ya amince Iran zata cigaba da habaka makamashin Uranium.

Sai dai kuma kasashen yamma sun ce, ba haka yarjejeniyar take ba.

Tuni kuma Fra ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yace, abinda aka cimma wani babban kuskure ne, kuma Isra'ila ba zata mutunta yarjejeniyar ba.

Karin bayani