Kiki-kaka kan kasafin Kudin Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption 'Yan adawa a Najeriya sun zargi gwamnati da jan kafa wajen gabatar da kasfin kudi

A Najeriya, gwamnatin kasar ta musanta cewa tana jan kafa game da batun gabatar wa 'yan Majalisun dokoki kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa.

Haka kuma gwamnatin ta musanta cewa kashi 40 cikin 100 na kasafin kudin shekarar da ke karewa ne kawai ta iya aiwatarwa ya zuwa yanzu.

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan jam'iyyar adawa a Najeriyar suka soki gwamnatin kasar da rashin gabatar da kasafin kudi na badi akan lokaci.

Sai dai Minista a ma'aikatar kudi ta Najeriyar Dr. Yarima Ngama, ya ce za'a gabatar da sabon kasafin kudin kasar na badi da zarar an samu daidaito tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai, dangane da batun kayyade farashin gangar mai.

Karin bayani