'Zargin baiwa 'yan majalisar Ghana cin hanci'

Image caption Shugaba John Mahama na Ghana

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a Ghana sun soki 'yan majalisar dokokin kasar bisa zargin sun karbi toshiyar baki daga wani kamfani na kasar China mai suna ZTE.

Kungiyoyin na zargin cewar 'yan majalisar sun karbi 'na goro' daga wajen kamfanin don su amince da wata babbar kwangilar tsakanin kamfanin da gwamnatin kasar.

Wasu rahotanni sun nuna cewar kamfanin ZTE ya baiwa 'yan majalisar wayoyin salula don sun amince da kwangilar kusan dala miliyan 130.

Wannan kwangilar dai ta kayayyakin sadawar ta shafin abubuwan dake da nasaba da tsaron kasar ta Ghana.

Karin bayani