Farashin mai ya fadi saboda Iran

wurin hakar man Iran
Image caption Iran ce ta hudu a duniya a kasashe masu arzikin mai

Farashin mai ya fadi da fiye da dala biyu a kan kowace ganga yayin da ake sa ran yarjejeniyar da aka cimma da Iran za ta ba ta damar sayar da karin mai.

Sai dai shugabar Hukumar Makamashi ta Duniya Maria van der Hoeven ta ce da wuya Iran ta dawo da fitar da yawan manta kamar da cikin sauri.

Ko da kuwa an janye dukkanin takunkumin da aka sanya mata na fitar da mai.

Masu lura da al'amura sun ce da wuya a kyale kasar ta kara yawan man da take sayarwa sosai cikin watanni shida.

A shekaru biyu da suka gabata takunkumin da aka sanya wa kasar ya kawo mata cikas wajen fitar da manta.

Karin bayani