An rufe rumfunan zabe a kasar Mali

Zabe a kasar mali
Image caption Zabe a kasar mali

An rufe rumfunan zabe a kasar Mali bayan da aka kammala kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki cikin lumana.

Zaben wani bangare ne na yunkurin dawo da dokar tsarin mulki, bayan da mamayar masu kaifin kishin Islama ta tilasta kasar Faransa daukar matakin soji a kasar cikin farkon wannan shekarar.

Sai dai jama'a basu fito kada kur'ar ba sosai, idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasar da aka gudanar watanni ukun da suka gabata .

Mutane da dama da suka kaurace zaben sun shaidawa BBC cewa ba su ji dadin yadda aka shirya zaben ba.

Wasu sun ce sun lura da yunkurin da wasu wakilian jam'iyu ke baiwa jama'a kudi don su kada kuri'a, suna mai cewa kasar bata shirya wa zaben ba saboda har yanzu 'yan tawaye abzinawa na rike da ikon wasu sassan arewacin kasar.

Amma kuma masu sa ido kan zaben na kasashen Turai da Afirka da ake sa ran zasu mika rahotonsu nan da ;yan kawanaki sun yi na'ama da yadda zaben ya gudana, tare da cewa zasu bayyana shi a matsayin mai inganci.