Najeriya: Kananan Jiragen sama sun janye yajin aiki

Image caption Da ma Kungiyar ta ce kananan jiragen ba za su ci gaba da jigilar fasinjoji ba har sai gwamnatin ta janye harajin.

Kungiyar masu kananan jiragen sama a Naijeriya ta janye yajin aikin da masu kamfunnan zirga-zirga jiragen saman a cikin kasar suka shiga a makon jiya.

Kungiyar ta kira yajin aikin ne bayan da Hukumar Kula da Sararin Samaniyar kasar ta fito da wani sabon harajin dala 3,000 zuwa 4,000 kan kowane tashin da karamin jirgi zai yi zuwa wani sashe na kasar.

Janyewar dai ta biyo bayan ganawar da kwamitin kula da harkokin sufarin jiragen sama na Majalisar Dattawan kasar ya yi da masu-ruwa-da-tsaki a harkokin zirga-zirgar kananan jiragen saman.

'' Masu kananan jiragen a Najeriya sun amince da komawa bakin aikin ne bayan wani zaman sasantatwa a kan dakatar da karbar duk wasu kudaden haraji.'' in ji wani wakilin BBC a Legas.

Karin bayani