Me yasa ba a samun lantarki a Kano?

Image caption Shugaba Nigeria Goodluck Jonathan

Kasa da wata daya da gwamnatin Nigeria ta mika wa 'yan kasuwa da suka sayi kamfanonin rarraba wutar lantarkin kasar, wasu kamfanonin sun fara kokawa da rashin cika alkawari wajen basu adadin wutar da za su rarraba.

Kamfanin Sahelian Energy da ya sayi kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano, ya ce adadin wutar da yake samu daga gwamnatin Nigeria ya gaza wanda suka yi yarjejeniya tun da farko, abin dake nan yasa jihohin da suke samun wuta daga yankin ke fuskantar karancin wuta.

Shugaban kamfanin, Dr Jameel Isyaku Gwamna ya ce " Yarjejeniyar da muka yi da gwamnatin Nigeria shine za a dinga bamu kashi takwas cikin dari na adadin wutan lantarkin da kasar ke samarwa, amma kuma a yanzu muna samun kasada kashi uku ne cikin dari a don haka ba zamu iya biyan bukatun jama'a ba."

BBC ta yi kokarin jin ta bakin ma'aikatar makamashin Nigeria amma an kasa samun jami'anta na wayar salula.

Matsalar karancin wutan lantarki a Nigeria dai ta dade tana janyo nakasu a kan harkokin ci gaban masana'antun kasar.

Karin bayani