Amirka na son ganin bayan Bashar Assad

Shugaba Bashar al-Assad na Syria
Image caption Shugaba Bashar al-Assad na Syria

Amirka ta kara jaddada cewa, ya kamata batun kawar da shugaba Assad na Syria daga karagar mulki, ya kasance abinda za a mayar da hankali a kai a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya za ta shirya a Geneva a watan Janairu mai zuwa.

A cewar wani kakakin fadar White House, Josh Earnest, taron shine zarafi mafi a'ala na kafa gwamnatin wucin gadin Syriar, da kuma kawo karshen wahalar da jama'ar kasar ke sha.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce za a fara sabon zagayen tattaunawar shirin zaman lafiya a kan rikicin Syria a birnin Geneva, a ranar 12 ga watan Janairu.

Mr Ban ya ce zai kasance abin da ba za a taba yafewa da shi ba, kuma kin yin amfani da wannan dama wajen kawo karshe wahalhalun da jama'ar Syria ke fuskanta.

Sanarwar musamman da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar bai baiyana cewa ko Iran babbar mai marawa shugaba Assad baya za ta halarci taron ba.

'Yan adawar Syria dai sun dage cewa sai shugaba Assad ya sauka daga mulki kafin a fara dukkan wata tattaunawa.

Can kuma a Syria, mayaka 160 ne suka mutu bangaren 'yan tawaye da kuma dakarun gwamnatin cikin kwanaki biyu sakamakon artabu a Damascus.

Karin bayani