'Mata na fuskantar azabtarwa a Syria'

Image caption A kan haka Ministan harkokin wajen Burtaniya ya ce dole ne a shigar da mata cikin taron samarda zaman lafiya a Syria da za a yi a birnin Geneva.

Wani rahoto da wata gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama 60 suka fitar ya nuna cewa mata a Syria na ci gaba da fuskantar hare-haren cin zarafi da azabtarwa daga dakarun gwamnati da kungiyoyin mayaka.

Rahoton ya yi kiyasin cewa daga fara rikicin kasar kawo yanzu mata 6,000 ne aka yiwa fyade daga ciki har da inda gungun mutane ke yiwa mace guda fyaden.

An gano hakan ne a wurin matan da abin ya shafa da kuma ma'aikatan asibitoci da aka yi hira da su a tsakiyar shekara ta biyu da fara rikicin Syria.

Rahoton ya kuma gano cewa ana ci gaba da samun misalai inda masu harbi a boye ke amfani da mata da yaransu a matsayin garkuwa baya ga yadda ake sace matan tare da yin garkuwa da su don musayar fursunoni ko daukar fansa.

Karin bayani