Rudani a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

'yan tawayen Seleka
Image caption Tun farkon watannan Mr Ban Ki-moon ya ce rikicin tsakanin al'ummomin kasar ka iya baci

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya tana tsunduma cikin mummunan rikici in ji mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya.

Jan Eliasson wanda yayi gargadin ya bukaci kwamitin tsaro na majalisar ya karfafa dakarun tabbatar da zaman lafiya na Afrika a kasar.

A kuma mayar da dakarun karkashin aikin tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Tuni tsohuwar mai mulkin mallakar kasar ta Afrika ta tsakiya Faransa ta yi alkawarin ba da karon sojoji 1000 ga dakarun.

Kuma a yanzu tana da sojoji 400 da ke babban birnin kasar Bangui domin kare 'yan kasar Faransa.

Image caption Mr Eliasson ya ce ana samun karuwar cin mutuncin mata da azabtarwa da kisan gilla da rikicin musulmi da kiristoci

Mr Eliasson ya ce kasar na zama wurin renon masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin masu gwagwarmaya da makamai a yankin da ke fama da rikici.

Kuma yara da mata su ne suka fi fuskantar hadari a rikicin.

A mako mai zuwa ne ake saran kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya zai amince da shawarar ba da izinin tura dakarun Afrika kasar da tallafin Faransa.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta fada rikici ne tun lokacin da 'yan tawaye suka kwace mulki a watan Maris.

Kungiyar 'yan tawayen ta Seleka ta maye gurbin shugaban kasar Francois Bozize da shugabanta Michel Djotodia.