Zargin maita a Ghana ya zama alheri

Paul Apowida
Image caption A kwanannan aka wallafa littafinsa kan batun camfa yara da maita

Paul Apowida sojan Birtaniya ne kuma kwararren mai zane ne wanda aka nemi halaka shi yana jariri saboda zargin maita a kauyensu na Sirigu a arewacin Ghana.

Allah ya azurta shi da basira Ko da ike kiris ya rage a hallaka shi lokacin yana jariri.

An yi yunkurin kashe shi ne a lokacin saboda an camfa shi da maita.

An yi hakan ne kuwa saboda jim kadan da haihuwarsa iyeyensa da wasu danginsu shida suka mutu.

Kauyen Sirigu da ke arewacin Ghana kusa da iyakar Burkina Faso nan ne kauyensu.

Bayan yunkurin ba shi guba domin hallaka shi ne wata malamar coci ta kai shi wani gidan marayu a kudancin kasar ta Ghana.

A karshe dai Paul Apowida ya zama dan Birtaniya inda ya shiga sojan kasar har yayi aiki a Afghanistan.