Rashin lantarki na barazana ga rayuwa a Gaza

Ramin karkashin kasa na satar shigar da kaya Gaza
Image caption Rufe irin wadannan ramuka ta kara haddasa matsalar rashin kayan jin dadin rayuwa a Gaza

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce matsalar dauke wutar lantarki a Gaza na barazana ga rayuka.

Ya ce rashin wutar lantarki a asibitoci ya sa dole ma'aikata su yi amfani na'urar samar da iska ta hannu domin ceton lafiyar jarirai sabbin haihuwa.

Jami'in Richard Falk, ya ce yawan dauke wutar ya kara tabarbara al'amura ta yadda ba a samun gudanar da muhimman ayyukan jin dadin jama'a.

Ya ce babban abin da ya haifar da matsalar shi ne rufe hanyoyin karkashin kasa da ake satar shigar da kayayyaki daga Masar da kuma rufe hanyoyin da Israela ta yi zuwa Gaza