An kashe mutane 37 a Filato

Image caption Jami'an tsaro na sintiri a jihar Filato

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa an kashe mutane fiye da talatin a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kan wasu kauyuka dake karamar hukumar Barkin Ladi.

Lamarin dai ya faru ne a kauyukan Gura-Bwok, da Fan da Heipang da kuma Foron.

An kai harinne a ranar Litinin da daddare da kuma safiyar Talata.

Rahotanni sun ce maharani dauke da bindigogi sun bude wuta ne babu kakkauwatawa a kan mazauna kauyukan a kusan lokaci guda, kuma Mrs Fatima Njokwu, jami'a a kungiyar kare muradun kirista ta Stefanos Foundation, ta shaidawa BBC cewa an kashe mutane talatin da biyu ne a duka kauyukan.

Wannan hari dai ya zo kimanin mako guda bayan da wasu 'yan bindigar da Fulani makiyaya ke zargin 'yan kabilar Berom ne suka kaddamar da hari a kan makiyaya suka sace shanu fiye da dari, suka kashe makiyaya hudu, ciki har da wasu biyu da 'yan bindigar suka kwace daga hannun jami'an tsaro suka kashe su yayin da suke wa jami'an tsaron rakiya domin kokarin karbo shanun da aka sace.

Jihar ta Filato dai ba bakuwa ba ce ga tashe-tashen hankula da wasu lokutan a kan danganta da kabilanci da addini da kuma siyasa inda aka samu hasarar dimbin rayuka.

Karin bayani