Yunkurin samun 'yancin kan Scotland

Image caption Tutar Scotland na kokarin samun 'yanci

Jagoran gwamnatin yankin Scotland, Alex Salmond ya kaddamar da manufofin gwamnatinsa na samun 'yancin kai, yana mai bayani dalla-dalla kan irin yadda yankin na Scotland zai yi aiki bayan ballewarsa daga Birtaniya.

Mr Salmond ya ce kasar Scotland mai 'yanci za ta rika tara harajinta, sai dai zat a ci gaba da amfani da takardar kudin fam na Ingila a matsayin kudinta, sannan kuma su ci gaba da daukar Sarauniya a matsayin shugabar kasarsu, kana su ci gaba da kasancewa a kungiyar Tarayyar Turai.

A badi ne al'ummar yankin Scotland za su kada kuri'ar raba-gardama kan ko zasu ci gaba da kasancewa a karkashin Birtaniya.

Kuri'ar jin ra'ayi dai na nuna cewa galibinsu sun fi goyon bayan hakan.