An tsare Dokubo-Asari a Jamhuriyar Benin

Image caption Alhaji Mujahid Dokubo-Asari

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin, har yanzu suna ci gaba da tsare tsohon shugaba wata kungiyar gwagwarmaya a yankin Niger Delta Alhaji Mujahid Dokubo-Asari.

Lauyan Mr Dokubo, Barrister Festus Keyamo a wata budaddiyar wasika da ya rubutawa Shugaba Goodluck Jonathan, ya ce 'yan sanda a Cotonou sun kama Asari Dokubo daga misalin karfe daya zuwa biyu na ranar Talata.

A cewar Lauyan, basu san abinda yasa aka tsare Dokubo ba, duk da cewar yana gudanar da halattatun kasuwancinsa kasar Benin din, inda yake da gidaje da makarantu a kasar.

Jami'an tsaro dai a Benin sun gudanar da bincike a kan gidajen Dokubo kuma ba su ga wani abu da ya sabawa doka ba.

Lauyansa, na zargin tsare Dokubo-Asari na da nasaba da kawancen dake tsakanin gwamnatin Benin da ta Nigeria a yayinda ake fuskantar zaben shekara ta 2015 a Nigeria.

Karin bayani