Jihar Imo ta soke iznin gidajen Marayu

Image caption Wakilin BBC a yankin ya ce akan killace 'yan matan da suka yi cikin shege a irin wadannan gidajen domin idan sun haihu a sayar da jariran.

Hukumomin Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun soke takardun izinin gudanar da ilahirin gidajen renon marayu da na renon jarirai da ke jihar.

Wannan dai ya biyo bayan yawaitar matsalar nan ta hada-hadar sayar da jarirai, wadda ake fama da ita a jihar da ma sauran wasu sassan shiyar ta kudu maso gabashin Najeriya.

''Gwamnatin jiha ta gano cewar ana aikata wasu haramtattun ayyuka wadanda kuma zan iya kira na fasadi a gidajen marayu da ke wannan jihar; kuma hakan ya zame wa wasu mutane wata hanyar safarar yara kanana a fakaice,'' inji Dr. Theodore Okechukwu, Kwamishinan Watsa Labarai na jihar.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce daga bisani za ta tantance wadannan gidajen reno, kuma ta yi masu wata sabuwar rajista don ganin ba su zama wuraren da ake samar da jariran da ake sayarwa ba.

Karin bayani