Gwamnonin da suka balle za su dawo - PDP

Image caption Shugaban PDP, Alhaji Bamanga Tukur

Jam'iyyar PDP mai mulki a Nigeria ta maida martani game da hadewar 'yan sabuwar PDP da jam'iyyar adawa ta APC.

A cewar PDP din matakin bai girgizata ba kuma daga karshe gwamnoni da suka balle zasu dawo.

Mataimaki na musamman ga shugaban Jam'iyyar PDP, Sanata Abubakar Umar Gada ya shaidawa BBC cewar " an samu ci gaba mai kyau saboda tafiyarsu kuma muna murna da haka".

"Ina tabbatar muku cewar da kansu zasu dawo, saboda mataimakin shugaban kasa ya taba barin PDP kuma da kansa ya dawo," in ji Gada.

A ranar Talata gwamnoni biyar daga cikin bakwai da suka bijire ma uwar jam'iyyar ta PDP suka sauya sheka suka hade da babbar jam'iyyar adawa ta APC.

Sun bayyana shawarar ne a wani taro da su ka yi, inda su ka ce sun dauki matakin ne saboda la'akari da cewa manufofinsu guda ne, na kawo sauye-sauye ga yadda ake gudanar da mulki a Nigeria.

Sai dai bisa dukkan alamu an samu baraka a 'sabuwar' PDPn saboda Gwamnan jihar Niger, Muazu Babangida Aliyu ya ce bai hade da APC ba.

Sannan kuma wata majiya mai tushe ta bayyana cewar shima gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido yananan a cikin PDP.

Karin bayani