An tsare wasu musulmi a Rasha

Musulmi a Rasha
Image caption An kama mutanen ne a wani samame da aka kai da sanyin safiya a gabashin birnin.

'Yan sandan Rasha sun ce suna tsare da wasu masu kaifin kishin Islama su goma sha biyar a Masko, babban birnin kasar.

Sun kuma kwace bamabamai hadin gida da nakiyoyi da kuma bindigogi.

'Yan sandan sun ce mutanen 'yan kungiyar nan ce ta At Takfir wal Hijra, wadda aka kafa a Masar a shekarun 1960, da aka haramta a 2010.

An tsaurara matakan tsaro a kasar ta Rasha ne watanni biyu kafin fara gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu a garin Sochi da ke gabar tekun Bahar Aswad.