'Ya kamata a sauya dokokin kaura a Turai'

Image caption Za a dai dage haramcin da aka saka wa 'yan Bulgariya da 'yan Romania na shiga Burtaniya a karshen shekaran nan

Firai Ministan Burtaniya ya yi kiran a fito da dokokin da za su hana mutane kaura daga wannan kasar Turai zuwa waccan ba tare da tambaya ba; abin da wani sharadi ne a yarjejeniyar kafa Tarayyar Turai.

A cikin wani sharhi da ya rubuta wa jaridar Financial Times, Mr. Cameron ya ce wannan sharadin ne musabbabin kaurar dimbin al'ummomi zuwa Turan, yana mai cewa lokaci ya yi na sake sabon lale.

Ya ce Tarayyar Turai na bukatar sauye-sauye in har ana son dawo da amincewar da mutane suka yi mata, yana mai nuni ga irin damuwar da ake da a Burtaniya game da ko mutane nawa zasu iya shigowa kasar daga Romaniya da Bulgaria bayan an janye haramcin shigarsu kasar a watan Janairu.

Mr. Cameron ya ce Burtaniya za ta takaita 'yancin baki 'yan kasashen waje na neman wasu hakkokin da ake ba ma'aikata kuma wadanda duk aka kama suna kwana a wuraren da basu dace ba ko suna bara, za a taso keyarsu daga kasar.

Karin bayani