'Lalura ce ta sa aka kashe wasu matasa a Apo'

Ginin majalisar dokokin Najeriya
Image caption Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun lashi takobin ganin sai anyi adalci akan lamarin

A Najeriya wani kwamitin da majalisar Dattawan kasar ta kafa don binciken kisan da aka yi wa wasu matasa takwas a unguwar Apo da ke Abuja , bisa zargin 'yan Boko Haram ne, ya ce larura ce ta sa jami'an tsaron budewa matasan wuta.

A cikin rahotonsa, kwamitin ya ce bincikensa ya gano cewa babu gaskiya a zargin da ake yi cewa kisan-gilla jami'an tsaron suka yi wa matasan.

Sai dai wasu daga cikin 'yan kwamitin sun soki rahoton, suna zargin cewa kwamitin ya fita daga hurumin aikin da aka ba shi na kokarin tattabatar ko matasan da aka kashe na da alaka da kungiyar Boko Haram.

An kashe mutanen takwas ne dai a ranar 20 ga watan Satumba a lokacin wani samame da jami'an tsaro suka kai a kan wani gida da ba'a karasa gininsa ba, wanda kuma mutanen ke kwana a cikinsa.

Karin bayani