EU ta gargadi Ukraine kan cinikayya

Image caption Shalkawatar kungiyar EU

Kungiyar tarayyar Turai ta gargadi Ukraine cewar tana kasada da makomar tattalin arzikinta, ta hanyar yin watsi da wata yarjejeniyar cinikayya ba tare da shinge da kungiyar ba domin son yin dangantakar kut da kut da Rasha.

Gargadin daga Kwamishinan kula da fadada kungiyar tarayyar Turan, ya zo ne sa'o'i kafin soma wani taron koli a Lithuania, wanda yake da aniyar zama karshen kokarin da aka dade ana yi don hada tsaffin kasashen tarayyar Soviet cikin kasashen yammacin duniya.

Wani tsohon Shugaban majalisar dokokin Turai wanda a halin yanzu yake jagorantar tawagar sa ido a Ukraine -- Pat Cox - ya ce yana fatan daga karshe Ukraine za ta yanke shawarar hada kanta da Turai.

'Zanga-zanga a Kiev'

Masu zanga zanga a Kiev babban birnin Ukraine na ci gaba da sa matsin lamba a kan gwamnatinsu, yayinda shugaba Yanukovych ya isa wajen taron koli a Lithuania.

Mutane kusan dari daya sun yi wata jana'izar wasa game da damar Ukraine ta hadewa tare da kungiyar tarayyar Turai.

Sun dauki wata makara lullube da wata tuta mai launuka daban daban zuwa Ofishin kungiyar tarayyar Turai dake a Kiev, tare da aje furannin kallo a wurin.

Karin bayani