Ma'aikatan Nokia sun kirkiri waya

Wayar Jolla
Image caption Wayoyin Jolla 450 aka samar a lokacin kaddamar da ita

Wata kungiyar tsofaffin ma'aikatan kamfanin Nokia ta fitar da wata wayar salula da ke amfani da wani sabon dandamalin wayar komai-da-ruwanka.

Wayar ta Jolla (da sautin Yolla ake furatawa) na amfani ne da tsarin Sailfish, amma za ta iya aiki da akasarin ire-iren masarrufar da aka yi don tsarin Android na Google.

Kamfanin ya hada gwiwa da wani kamfanin sadarwa na Finland, yana kuma fatan kulle wata yarjejeniya da wani kamfani na Birtaniya.

Masharhanta a bangaren sadarwa sun ce wayar ta Jolla na fuskantar kalubalen samun gurbi a kasuwar da tuni Google da Apple suka yi kaka-gida.

Kamfanin Nokia ne dai ya kirkiri tsarin da wayar ke amfani da shi (wanda a da ake kiransa MeeGo) amma ya yi watsi da shi a shekarar 2011.