Jihar Kano ta lalata dubban kayan maye

Sarkin Kano Dr. Ado Bayero
Image caption Jihar ta Kano dai ita ce tafi adadi mafi yawa na matasa masu amfani da kayan maye da kuma miyagun kwayoyi a Najeriya.

Jami'ai a jihar Kano ta Najeriya sun lalata dubun dubatar kayan maye da suka kwace daga masu ta'ammuli dasu a lokutta daban-daban.

Kayayyakin dai sun hada da barasa da tabar wiwi da kuma sanadarin 'sholisho'.

Hukumar Hizbah mai kula da tabbatarda aiki da tsarin Shari'ar Musulunci a jihar wadda ita ce ta kama kayan, ta gudanar da aikin lalata kayan mayen ne bayan wata kotun Islama ta yanke hukuncin cewa wajibi ne a lalata su.

'' Wannan hukumar ta Hizbah ta yi nasara wajen kama giya kwalba 244,151 da tabar wiwi wadda ta kai kulli 320,000 da kuma sholiso wanda ya kai kwaya 42,386'' inji Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa kwamandan hukumar.

Karin bayani