Afghanistan ta gargadi Amurka

Hamid Karzai
Image caption Akwai sabani tsakanin Amurka da Hamid Karzai kan lokacin sanya hannu akan yarjejeniyar

Wani mai magana da yawun shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce Afghanistan ba za ta sa hannu a yarjejeniyar tsaro da Amurka ba sai an daina kai harin sama kasar.

Kakakin ya yi gargadin cewa dole ne sojojin kasashen duniya da suke Afgahistan su dena kai hare haren ta sama indai ana son amincewa da yarjejeniyar.

Ya furta hakan ne kwana daya bayan da sojojin NATO suka kai hari ta sama lardin Helmond.

Harin da hukumomin yankin suka ce ya kashe wani yaro ya raunata wasu mata biyu.

A wata sanarwa da ta fitar NATO ta ce ta yi nadamar duk wata mutuwa ko jikkata da aka samu ta farar hula.

Yarjejeniyar tsaron dai ta tanadi ci gaba da zaman sojojin Amurka aAfghanistan har bayan 2014 lokacin da akasarin sojojin kasashen duniya za su fice daga kasar.