Bam ya kashe mutane 40 a Libya

Wasu 'yan tawayen Libya
Image caption Har yanzu ba kwanciyar hankali a Libya tun bayan hanbarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi.

Rahotanni daga kasar Libya na cewa wani hari da aka kai inda ake ajiye makamai a kasar ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane arba'in.

Wani jami'in tsaro ya ce lamarin ya faru ne a kusa da birnin Sabha a lokacin da wasu gungun 'yan cirani 'yan Afrika ke kokarin satar makamai.

Asibitin yankin dai na kokarin kulawa da wadanda suka ji rauni.

Tun da fari wasu sojoji hudu sun rasa rayukansu a Bengazi ya yin wani fada da masu kaifin kishin islama.

Karin bayani