Nigeria: An yi wa dan Lebanon daurin rai-da-rai

Image caption An kama 'yan Lebanon din ne bayan an gano wani gida makare da bama bamai a Kano

Wata babbar kotu a Abuja da ke Nigeria ta yankewa wani dan kasar Lebanon, Tahal Roda, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan ta same shi da laifin aikata ta'addanci.

Kotun ta kuma wanke wasu 'yan kasar ta Lebanon, Mustapa Fawaz da Abdullahi Thani, daga zargin aikata ta'addanci.

Sai dai lauyoyin Tahal Roda sun ce mai yiwuwa zai daukaka kara.ria court

An dai kama 'yan kasar ta Lebanon ne bayan da aka gano wani gida a jihar Kano makare da makamai, wanda kuma aka ce na mutanen ne.

Karin bayani