An soma shari'a kan kashe soja a Woolwich

Image caption Lee Rigby

Masu gabatar da kara a wata kotu a London sun yi cikakken bayani na kisan wani sojin Birtaniya da aka yi cikin watan Mayun da ya wuce a kusa da Barikinsa.

Dukkanin mutanen biyun da ake zargi da kisan, Michael Adebowale da Michael Adebolajo sun musanta tuhumar.

A cikin bayaninsa na soma shara'ar,mai gabatar da kara ya ce mutanen biyu sun banke sojin,Lee Rigby da mota sannan suka ja shi kasa rai kwakwai mutu kwakwai har zuwa tsakiyar titi, ta yadda masu wucewa za su iya ganinsa.

Daga nan sai suna datse shi ya mutu da wukake, sannan suka yi kokarin sare kan.

Mutanen biyu ba su gudu ba, sannan daga bisani suka kai kari a kan wata motar yansandan da suka je wurin.

Karin bayani