Jirgin sama ya fadi a Glasgow

scotland
Image caption Mashayar da jirgin sama ya fadi a Glasgow

Ana cigaba da aikin ceto a birnin Glasgow na Scotland bayan wani jirgin sama mai saukar Ungulu na 'yan sanda ya fada kan wata mashaya dake cike da mutane.

'Yan sanda dai sun ce mutane da dama sun jikkata, amma ba su bayar da karin bayani ba.

Ma'aikatan ceton na kokarin kaiwa ga mutane da dama da aka rutsa da su cikin ginin wanda suka ce halin da yake ciki na da matukar hadari.

Mutanen da suka shaida lamarin sun ce sun ga lokacinda jirgin yake wucewa ta saman gidan giyar dake tsakiyar Glasgow kafin ya fado kamar dutse.

'Yan sanda sun ce mutane uku ne ke cikin jirgin ,yayinda mutane 120 ke cikin mashayar lokacin da lamarin ya faru.