'Mutane 33 sun mutu a hatsarin jirgin sama'

An gano burbushin jirgin saman fasinja na Mozambique Airlines da ya bace dauke da mutane 33. An gano jirgin ne a gandun daji dake arewa maso gabashin Namibia.

'Yan sandan Namibia ne dai suka gano burbushin jirgin da ya kone kurmus a wani gandun daji. Kuma 'yan sandan sun ce ba wanda ya tsira daga hatsarin.

An dai shafe sao'i da dama kafin a kai ga gano hakikanin abinda ya faru da jrigin saboda ya fado a ne tsakar daji, kuma babu titunan da suka ratsa wurin.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ma ya kawo tsaiko wajen kaiwa inda jirgin ya fadi.

Yawancin fasinjan dake cikin jirgin dai 'yan kasashen Mozambique ne da kuma Angola.

Akwai kuma 'yan kasashen Portugal, Faransa, da Barzil da kuma China.