wani jirgin sama ya bata a Mozambique

Wani jirgin sama na kasar Mozambique dauke da fasinjoji 28 da ma'aikatan jirgin 6 ya bace.

Jirgin wanda ya taso daga Mozambique zuwa Angola, ya taso ne daga Maputo amma bai isa Luanda ba babban birnin kasar ta Angola.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Mozambique ya ce bayanan farko da aka samu sun nuna cewar watakila jirgin ya sauka ne a arewacin Namibia.

Jami'ai kuma sun ce suna kokarin tuntubar hukumomi a can.